'Matakai hudu da NNPP za ta dauka don kawo tsaro a jihar Zamfara'
'Matakai hudu da NNPP za ta dauka don kawo tsaro a jihar Zamfara'
An wallafa
Dan takarar gwamna Jihar Zamfara a jam’iyyar NNPP ya ce ya fito takara ne domin yin amfani da basirarsa wajen alkilta arzikin da Allah ya huwace wa jihar.
Farfesa Kabir Umar Ja-Baka ya ce zai fi mayar da hankali kan abubuwa guda hudu da suka hada da inganta tsaro da noma da ilimi da kuma sana’o’i.
Farfesa ya kara da cewa idan ya samu dama zai dauki matakai na musamman wadanda yanzu gwamnatoci suka gaza wajen inganta sha’anin tsaro.



