Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barazana 5 da duniya ke fuskanta a 2026 da yadda hakan zai shafi Afirka
Rashin tabbas na ƙara yin ƙamari a tsakiyar yanayin duniya, a cewar rahoton da ke bayani kan barazanar da duniya ke fuskanta na 2026 na taron ƙolin tattalin arziƙi na duniya wanda aka wallafa a ranar 14 ga Janairu, 2026.
A wannan bugu na 21, taron ƙolin ya yi gargaɗin cewa duniya na ƙara shiga wani yanayi da ke tattare da rikice-rikice, rarrabuwar kawuna, da kuma raguwar haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.
Bisa ga amsoshin ƙwararru sama da 1,300 da aka tattara a cikin binciken 2026, rahoton ya tantance hadurran da ake sa ran za su fi yin tasiri ga kamfanoni a cikin shekaru masu zuwa.
A cikin shekaru biyu masu zuwa, kashi 50 cikin 100 na waɗanda aka tambaya sun yi hasashen cewa yanayin duniya zai kasance "mai cike da tashin hankali" ko "mai kama da hadari", idan aka kwatanta da kashi 42 cikin 100 a shekarar da ta gabata.
A wannan sabon "zamanin gasa da juna", wadanne ne manyan haɗurra guda biyar da ake ganin za su fi tsanani zuwa shekarar 2028? Kuma mafi muhimmanci, wane tasiri suke da shi ga Afirka?
1 - Rikicin tattalin arziƙi tsakanin ƙasashe
Wannan shi ne hadarin da aka sanya a matsayin na farko, duka nan da nan a shekarar 2026 da kuma a cikin shekaru biyu masu zuwa, wato zuwa shekarar 2028.
Wannan hadarin ya sauya daga matsayi na takwas idan aka kwatanta da bara.
Rahoton ya bayyana cewa ana samun karuwar amfani da matakan kariyar tattalin arziki kamar kakaba haraji kan kayayyakin shigo da kaya, sanya takunkumai kan zuba jari, kakaba wa kasashe ko kamfanoni takunkumi, da kuma raunin tsarin sasanta rikice-rikicen kasuwanci na Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO).
Rahoton ya kuma nuna cewa yawan kararrakin da ake shigarwa a wannan tsarin ya ragu da kusan kashi biyu bisa uku tun bayan dakatar da aikin Kwamitin Daukaka Kara na ƙungiyar kasuwancin ta duniya a shekarar 2019.
Ga Afirka, rahoton ya nuna manyan fannoni biyu da nahiyar ke da rauni kai tsaye a cikinsu:
- Gasar neman muhimman ma'adanai: Taron ƙoli na tattalin arziƙin duniya, WEF na hasashen cewa gwamnatoci za su ƙara tara ajiyar ƙarafa da ma'adanan da ake buƙata wajen sauyin tsarin makamashi mai tsafta. Hakan na iya haifar da matsin lambar kasuwanci, diplomasiyya ko ma ta soja kan ƙasashen da wadannan albarkatu suke. Wannan bayani ya shafi ƙasashen Afirka kai tsaye, musamman wadanda suke da arziƙin ma'adanan cobalt, lithium, tagulla da kuma sauran nau'ikan ma'adanai.
- 'Yancin cin gashin kai a harkar kuɗi: Rahoton ya nuna cewa ƙasashe masu tasowa da ke da kuɗaɗen ƙasar da ba su da karfi sun fi fuskantar haɗari daga yaduwar kuɗaɗen digital da aka daure darajarsu da kudaden kasashen waje. Ana hasashen yawan kudaden da ke cikin irin wadannan kuɗi na digital zai kai dala tiriliyan 1.22 nan da karshen shekarar 2028, idan aka kwatanta da dala biliyan 173 a karshen shekarar 2025. Wannan lamari na iya ƙara raunana ikon manyan bankunan kasashen Afirka wajen tafiyar da manufofin kudinsu, domin mutane na iya karkata zuwa amfani da wadannan kudaden dijital maimakon kudaden kasashensu.
2 - Yaɗa bayanan ƙarya da yaudarar jama'a
Wannan shi ne haɗari na biyu mafi tsanani da duniya za ta fuskanta a cikin shekaru biyu masu zuwa. Haka kuma, ya riga ya kasance a matsayi na huɗu cikin haɗurran da suka fi yiwuwar haddasa rikicin gaggawa a shekarar 2026.
Rahoton ya nuna cewa ana ƙara samun wahala wajen bambance tsakanin sahihin bayani da kuma bayanan da fasahar AI ta ƙirƙira, musamman fasahar bogi ta deepfakes wato bidiyo, hotuna ko sautukan bogi da suke kama da na gaske. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da amincewar jama'a ga kafafen yaɗa labarai na gargajiya ke raguwa.
Tasirin hakan ga Afirka
Ga Afirka, wannan na ɗaya daga cikin haɗurran da rahoton ya bayar da wani gagarumin ƙididdiga a matakin nahiyar:
- Kashi 73 cikin 100 na waɗanda aka tambaya a Afirka sun ce suna damuwa game da ikon su na bambance gaskiya da ƙarya a intanet.
- Wannan ya fi matsakaicin duniya na kashi 58 cikin 100 yawa.
- Adadin ya yi daidai da na Amurka, inda shi ma kashi 73 cikin 100 ke nuna irin wannan damuwa.
Rahoton ya kuma lura cewa Afirka na daga cikin yankunan duniya da amfani da kafafen sada zumunta a matsayin tushen labarai ke ƙaruwa cikin sauri. Wannan ba ya rage haɗarin yaɗuwar bayanan ƙarya, sai ma ya ƙara yawan mutanen da za su iya faɗawa cikin tasirinsa.
A takaice, ƙaruwa da amfani da kafafen sada zumunta tare da bunƙasar fasahar AI na iya sa ya zama mafi wahala ga mutane su gane sahihan bayanai. Wannan na iya shafar zaɓe, tsaro, zaman lafiyar al'umma da kuma amincewar jama'a ga hukumomi da kafafen yaɗa labarai a ƙasashen Afirka.
3 - Rarrabuwar kawunan al'umma
Wannan haɗarin ya tashi daga matsayi na ɗaya zuwa na uku a jerin manyan haɗurran da ake ganin za su fi tsanani nan da shekarar 2028.
Rahoton ya bayyana cewa wannan haɗarin yana da alaƙa ta kusa da haɗarin da ya gabata na yaɗa bayanan ƙarya da bayanan yaudara. Bayanai marasa inganci na ƙara rarraba al'umma zuwa ɓangarori daban-daban, yayin da wannan rarrabuwar kawuna ke ƙara raunana amincewar jama'a ga hukumomi da cibiyoyi, tare da rage ikon al'umma na haɗa kai domin tunkarar matsaloli da rikice-rikice.
Dangane da Afirka, rahoton bai bayar da takamaiman ƙididdiga ga wannan haɗarin ba. Sai dai tsarin da ya bayyana yana da alaƙa kai tsaye da abin da aka gano game da yaɗa bayanan ƙarya, wanda shi ne haɗari na biyu a jerin.
Rahoton ya nuna cewa:
- Tsarin umarni na kwamfuta wato algoritim ɗin kafafen sada zumunta kan riƙa nuna wa masu amfani irin bayanan da suka fi dacewa da ra'ayoyinsu, lamarin da ke haddasa "bazuwar bayanai".
- Hakan kan sa mutane su riƙa mu'amala ne kawai da bayanan da suka yi daidai da ra'ayoyinsu, tare da rage fahimtar ra'ayoyin wasu.
- A lokaci guda, amincewa da cibiyoyin gwamnati, kafafen yaɗa labarai da sauran hukumomi na iya ci gaba da raguwa.
A Afirka, inda yawan masu amfani da intanet da kafafen sada zumunta ke ƙaruwa cikin sauri, tare da yadda mutane da yawa ke nuna damuwa kan amincin bayanan da suke gani a yanar gizo, akwai yanayi da zai iya ƙara haifar da wannan rarrabuwar kawuna.
Wannan na iya zama musamman a lokacin:
- Yaƙin neman zaɓe da zaɓuɓɓuka.
- Muhawarar manyan manufofin gwamnati
- Rikice-rikicen ƙabila, addini ko yanki
- Lokutan matsalar tsaro ko na tattalin arziki.
A taƙaice, ƙaruwa da rarrabuwar kawunan al'umma na iya sa ya zama mafi wahala ga ƙasashen Afirka su cimma matsaya guda kan muhimman batutuwan ƙasa, tare da raunana zaman lafiya, haɗin kai da ƙarfin al'umma wajen magance manyan ƙalubale.
4 - Matsanancin sauye-sauyen yanayi
Wannan shi ne haɗari na huɗu mafi girma da ake sa ran duniya za ta fuskanta nan da shekarar 2028. Amma idan aka duba shekaru goma masu zuwa, zuwa shekarar 2036, shi ne haɗarin da ya zo a matsayi na farko, abin da ke nuna cewa taron ƙolin tattalin arziƙi na kallon sauyin yanayi a matsayin babbar barazana ta dogon lokaci ga duniya.
Rahoton ya nuna cewa matsanancin al'amuran yanayi na ci gaba da lalata muhimman ababen more rayuwa, musamman a fannonin:
- Samar da ruwa
- Makamashi
- Sufuri da hanyoyin zirga-zirga
Rahoton ya kuma yi nuni da cewa lokutan fari na ƙara tsawaita a wurare da dama, lamarin da ke ƙara matsin lamba ga tattalin arziki da rayuwar jama'a.
Ga Afirka, rahoton ya jaddada wani muhimmin abu: illolin matsanancin al'amuran yanayi ga muhimman ababen more rayuwa za su fi tsanani a ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi ta fuskar tattalin arziki, domin suna da ƙarancin damar daidaita kansu da sauye-sauyen yanayin.
Rahoton ya ba da misalin Maroko a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da wasu cibiyoyin samar da wutar lantarki ta ruwa ke fuskantar barazanar zama kadarori ko ayyukan da suka daina yin amfani yadda aka tsara saboda tsawaitar fari. An kuma ambaci:
- China
- Jordan
- Iraq
- Syria
Saboda haka, rahoton ya nuna cewa duk da cewa Afirka ba ta da gagarumar gudummawa wajen haifar da sauyin yanayi idan aka kwatanta da sauran yankunan duniya, tana daga cikin yankunan da ba su da cikakken shiri ko ƙarfin da za su iya jure wa illolinsa.
Wannan na iya haifar da:
- Raguwar samar da abinci saboda fari da rashin tabbas na damina.
- Ƙarancin ruwa ga gidaje, noma da masana'antu.
- Matsaloli wajen samar da lantarki, musamman a ƙasashen da suka dogara da madatsun ruwa.
- Lalacewar hanyoyi, gadoji da sauran ababen more rayuwa sakamakon ambaliya da guguwa.
- Ƙaruwa a ƙaura da matsalolin jin ƙai yayin da mutane ke barin yankunan da bala'o'in yanayi suka shafa.
A takaice, rahoton taron ƙolin tattal;in arziƙin na duniya ya nuna cewa sauyin yanayi ba kawai matsalar muhalli ba ce, har ma babbar barazana ce ga ci gaban tattalin arziki, tsaron abinci, samar da ruwa da makamashi, musamman a Afirka.
5 - Rikicin makamai tsakanin ƙasashe
Wannan haɗarin yana matsayi na biyar cikin manyan haɗurran da ake sa ran za su fi tasiri a cikin shekaru biyu masu zuwa, wato zuwa shekarar 2028. Hakan na nuni da sauka da matsayi ɗaya idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, lokacin da yake a matsayi na farko cikin haɗurran da suka fi iya haddasa rikicin gaggawa.
Sai dai rahoton ya jaddada cewa wannan saukar matsayi ba yana nufin barazanar ta ragu ba.
A maimakon haka, haɗarin yana da alaƙa ta kusa da rikicin tattalin arziƙi tsakanin ƙasashe wanda shi ne haɗari na farko a jerin. Duk wani ƙarin tsanani a ɗaya daga cikinsu na iya ƙara rura wutar ɗayan.
Abin da hakan ke nufi ga Afirka:
Rahoton ya danganta wannan haɗarin kai tsaye da gasa ta duniya wajen mallakar ko samun damar amfani da albarkatun ƙasa masu muhimmanci.
Ya nuna cewa:
- Manyan ƙasashe na ƙara shiga kai tsaye ko a kaikaice cikin yankunan da ke da muhimmancin albarkatun ƙasa.
- Gasa tsakanin waɗannan ƙasashe na ƙara tsananta a wuraren da ake da ma'adanai da albarkatun da ake bukata a dabarun tattalin arziƙi da makamashi.
- Wannan yanayi ya shafi wasu yankunan da ke fama da rikici a Afirka kai tsaye, musamman inda ake da tarin ma'adanai da albarkatun ƙasa masu daraja.
Shin Afirka a shirye take?
Tambayar ita ce: shin Afirka za ta kasance cikin shiri domin fuskantar duniya inda:
- Manyan ƙasashe ke rage haɗin gwiwa da juna,
- Albarkatun ƙasa ke zama makamin faɗa da tasiri,
- Kuma bala'o'in sauyin yanayi ke ci gaba da ƙaruwa?
Rahoton WEF ya nuna cewa duk da cewa haɗurran siyasa da na ƙasa da ƙasa ne suka mamaye hasashen shekarar 2028, zuwa shekarar 2036 haɗurran muhalli na iya komawa kan gaba.
A lokacin, manyan barazanar za su haɗa da:
- Matsanancin al'amuran yanayi,
- Asarar halittu da nau'o'in rayuwa (biodiversity loss),
- Manyan sauye-sauye a tsarin halittar duniya.