Matashin da ya ƙera babur mai ƙafa uku a Kano

Matashin da ya ƙera babur mai ƙafa uku a Kano
An wallafa

Wani matashi ɗan Najeriya, Faisal Sunusi Mika'il ya bayyana fatan cewa hukumomi za su taimaka wajen bunƙasa fasaha da baiwar matasan ƙasar, ta yadda za su riƙa ƙere-ƙere da samar da kayan ƙirƙira masu amfani ga ɗan'adam.

Matashin wanda ya ƙera babur mai ƙafa uku ko a-daidaita-sahu, ya ce shi ne ya ƙera baburin tun daga tushe, bayan ya zana shi a kwamfuta, kafin ya duƙufa wajen ganin ya tabbata a aikace.

Ya ce ko da yake yana da baiwar ƙere-ƙere, amma dai ya yi amfani da fasahohin sadarwa na zamani kamar Youtube don inganta ilmi da fasahar da da yake yi.

Matashin ya ce babban burinsa shi ne Najeriya ta fara ƙera ababen hawan da al'ummarta za su yi amfani da su a cikin gida.

Faisal Tech