Gane Mini Hanya: Kan zaɓen shugaban ƙasar Ghana 3/11/2024
Yayin da zaɓen shugaban ƙasar Ghana ke ci gaba da ƙaratowa, masharhanta na ganin addini zai iya tasiri kan yadda ƴan ƙasar za su jefa ƙuri’a fiye da kowane lokaci a baya.
A karon farko, za a ƙara ne tsakanin Kirista wanda ya fito daga tsatson Musulmi marasa rinjaye da kuma Musulmi wanda ya fito daga tsatson kiristoci masu rinjaye a ƙasar da ke fafutikar raba harkokin mulki da addini.
Jam’iyya mai mulki ta NPP a karon farko, ta tsayar da Musulmi Alhaji Mahmudu Bawumia a zaman ɗan takararta, yayin da babbar jam’iyyar adawa ta NDC ta tsayar da Kirista tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama.
A filin Gane Mini Hanya na wannan mako, Haruna Shehu Tangaza ya tattauna da Alhaji Ben Abdallah Banda jami’in gudanarwa a kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyya mai mulki ta NPP mai kula da zangonni.