Amsoshin Takardunku 23/02/2025

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Amsoshin Takardunku 23/02/2025
An wallafa

A filin na wannan mako za ku ji ko hukumar 'yansanda ta ƙasa da ƙasa wato Interpol aiki ɗaya take da hukumomin leƙen asiri ko kuma akwai bambanci.

Sannan a ɓangaren fasaha akwai bayani kan irin dabbobin da ake yin zare da gashi ko jijiyoyinsu.

A ƙarshe kuma za a ji bayanin likita kan yadda ake kamuwa da cutar hangum wadda ta fi kama yara, da illolinta da kuma yadda za a kare kai daga kamuwa da ita, duka cikin wannan shirin wanda Zulaihat Abubakar ta gabatar.