Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Sakamakon da Ghana ke samu abin kunya ne a wurinmu'
Ghana na daf da rasa damar halartar gasar nahiyar Afrika karon farko tun shekarar 2004, kuma yanzu haka ana ta ƙoƙarin yadda za a habbaka tawagar ta Black Stars.
Rashin nasarar da Ghana ta yi a hannun Sudan da ci 2-0 a ranar Talata ya sa tana matsayi na uku a rukunin neman shiga gasar nahiyar ta 2025 inda take da maki biyu kacal lokacin da ya kamata ya zama 12.
Kyaftin Mohammed Kudus ya nemi afuwa amma ƙoƙarinsu a neman shiga gasar da za a yi a Moroko na ci gaba da samun koma baya, kamar yadda aka riƙa cire su a matakin rukuni a gasar ta Afcon a shekarar 2021 da 2023.
"Tawagar ƙasarmu na fama da koma baya cikin shekaru biyar zuwa shida, kuma muna ta lalaɓa abubuwa," in ji tsohon ɗan wasan Ghana Emmanuel Agyemang-Badu a hirarsa da BBC.
"Muna gayawa kanmu gaskiya kuma ga inda muka samu kanmu.
"Tawagarmu ba ta buga wasan da ya kamata, in yau mun yi mai kyau gobe sai mu gaza. Muna wasa ne tamkar ba mu damu ba.
"Abin baƙin ciki ne da takaici a gare mu."
Mai horaswa Otto Addo, wanda ke ke jagorantar tawagar Black Star, ya zo ne lokacin da aka sanya mata ido saboda neman wanda zai iya gyara tawagar da a baya ta mamaye kwallon Afrika.
Ghana ta lashe kofin nahiyar Afrika sau huɗu a tarihi - inda ta ɗaga kofin a 1963 da 1965 da 1978 sai kuma 1982 - amma a yanzu wasa uku ta ci cikin 16 da ta buga a baya.