Kalvin Phillips: West Ham na son ta dauko dan kwallon Manchester City

An wallafa

West Ham na son dauko dan kwallon Manchester City da Ingila, Kalvin Phillips.

Phillip ya buga wasa 10 a kakar wasa ta bana tare da City kuma kungiyar na shirin sayar da shi a watan Janairun bana.

Baya ga West Ham akwai wadansu kungiyoyin kamar Newcastle da Juventus wadanda suma suke zawarcin dan kwallon.

Sai dai akwai wata matsala saboda City na bukatar makudan kudade domin bayar da aron Phillips din.

A watan Yulin 2022 ne City ta dauko Kalvin Phillips daga Leeds a kan fan miliyan 45.

Kocin West Ham David Moyes na son kara karfin tawagarsa saboda raunin da ya sa 'yan wasansa da dama suke jinya.

Lucas Paqueta da Michail Antonio na daga cikin wadanda ke jinya a West Ham sai kuma dan kwallon Mexico Edson Alvarez.