Lokaci bakwai mafi muhimmanci a rayuwar Shugaba Putin

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da Shugaban Rasha Vladmir Putin ke cika shekara 70 da haihuwa ranar Juma'a, mun duba yadda aka yi ya zama shugaban da duniya ta ware wanda ya ƙaddamar da mamaya kan Ukraine.
Lokaci bakwai masu miuhimmanci a rayuwarsa ne suka taimaka wajen sauya tunaninsa da kuma bayanin yadda yake ƙara adawa da Turawan Yamma.
Fara wasan kokawa na Judo a 1964

Asalin hoton, Getty Images
An haife shi a Leningrad, garin da ya fuskanci ƙofar rago tsawon kwana 872 yayin Yaƙin Duniya na Biyu. Putin ya kasance matashi majiyin ƙarfi a makaranta - wani babban abokinsa ya ba da labarin cewa "yana iya yin faɗa da kowa" saboda "ba shi da tsoro".
Yana shekara 12 ya fara samun horo a dabarun kare kai na martial art a turance, da kuma wasan kokawa na judo.
Ya samu ƙwarin gwiwa sosai, kuma ya zuwa lokacin da ya kai shekara 18 ya samu kambun gasar, har ma ya zama na uku a ƙaramar gasar a matakin ƙasa.
Tabbas ya yi ta amfani da wannan ƙwarewar wajen nuna mazantakarsa. Ya kuma koya masa cewa a irin wannan duniyar mai haɗari akwai buƙatar mutum ya samu ƙarfin gwiwa.
A cewarsa, idan faɗa ya zama dole, "ya zama dole ka fara kai naushi mai ƙarfi ta yadda abokin faɗanka ba zai iya tasowa ba".
Neman aiki da KGB a 1968
Akasarin mutane na guje wa zuwa 4 Liteyny Prospekt, ofishin siyasa na hukumar leƙen asiri ta KGB da ke Leningrad saboda tsananin horo da ma'aikata ke fuskanta.
Duk da haka, lokacin da yake shekara 16, Putin ya shiga farfajiyar ginin kuma ya tambayi wani ofisan da ke aiki a lokacin game da yadda zai iya samun aiki da su.
An faɗa masa cewa sai ya kammala horon soja ko kuma ya yi digiri, kuma nan take ya tambayi a wane fanni ya kamata ya yi digirin.
An ba shi shawarar ya karanta lauyanci, abin da ya sa ya mayar da hankali kuma aka ɗauke shi aikin bayan ya kammala.
Ya sha bayyana sha'awarsa ga yadda tasirin aikin yake - kamar yadda ya taba bayyana irin fina-finan leƙen asiri da ya dinga kallo yana matashi, "ɗan leƙen asiri ɗaya zai iya yanke wa dubban mutane hukunci".
Dandazon jama'a da suka kewaye shi a 1989
Duk da fatansa, aikinsa na KGB bai ɗore ba da kyau. Ma'aikaci ne kawai amma ba babba ba. Duk da haka ya gabatar da kansa a wajen koyon harshen Jamusanci, abin da ya sa ya samu damar aiki a ofishin KGB na Dresden a 1985.
A nan ya ci gaba da aiki a matsayin babban ma'aikaci, amma a Nuwamban 1989 ne gwamnatin Jamus ta Gabas ta fara rushewa cikin sauri.
A ranar 5 ga watan Disamba wani dandazon mutane ya kewaye ofishin KGB na Dresden. Cikin firgici Putin ya kira rundunar sojan ƙasar mafi kusa don neman kariya, inda nan take suka faɗa masa cewa " ba za mu iya yin komai ba sai an ba mu umarni daga Moscow kuma mun kasa samun Moscow a waya".
Nan da nan ya lura cewa abin tsoro ne idan gwamnati ta gaza - ya yi alwashin ba zai sake maimaita abin da yake ganin kuskure ne na Shugaba Mikhail Gorbachev na ƙin amsa kira da gaggawa yayin da 'yan adawa suka kewaye mutum.
Samar da shirin "sauya mai da abinci" a 1992
Jim kaɗan bayan haka Putin ya bar KGB kuma ya samu aiki a matsayin ɗan-jagora a ofishin magajin garin da ya zama St Petersburg a yanzu.
Tattalin arziki na cikin wani hali a lokacin, saboda haka aka ba Putin aikin taimaka wa mutanen garin farfaɗowa ta hanyar musayar man fetur da ya kai darajar dala miliyan 100 don samun abinci.
A bayyane dai ba wanda ya ga abincin, amma a cewar wani bincike, Putin da abokansa da kuma gungun matasa sun zuba kuɗin a aljihunsu.
A shekarun 1990, Putin ya fahimci cewa tasirin irin na siyasa abu ne da zai kawo kuɗi. A lokacin da kowane mutum ke amfana da matsayinsa, me zai hana shi ma ya amfana?
Mamaye Georgia a 2008
Lokacin da Putin ya zama shugaban Rasha a 2000, ya so ya gyara alaƙa tsakaninsa da ƙasashen Yamma - ta hanyar da yake so, ciki har da yaɗa tasirinsa a ƙasashe tofaffin mambobi a Tarayyar Soviet.
Ba daɗewa kuma ya fuskanci ɓacin rai, kuma ya yi fushi, yana tunanin ƙasashen Yamma na yunƙurin warewa da kuma ƙasƙanta Rasha.
Lokacin da Shugaban Georgia Mikheil Saakashvili ya nuna sha'awar saka ƙasarsa a cikin ƙawancen Nato, ran Putin ya ɓaci kuma yunƙurin da ƙasar wajen ƙwato yankin da ɓalle da ke samun goyon bayan Rasha ya jawo mata tsattsauran hukunci daga Rasha.
Cikin kwana biyar dakarun Rasha suka ragargaje rundunar sojan Georgia kuma suka tilasta wa Saakashvili saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Zanga-zanga a Moscow daga 2011 zuwa 2013

Asalin hoton, Getty Images
Imanin da mutane da yawa suka yi cewa an yi maguɗi a zaɓen 'yan majalisa na 2011 ya jawo zanga-zanga, wadda ta yi zafi bayan Putin ya sanar cewa zai sake tsayawa takara a 2012.
Macin da aka yi wa laƙabi da "Bolotnaya Protests" ya bayyana mafi girman zanga-zanga da aka taɓa yi a ƙarƙashin Putin a lokacin.
Ya yi imanin cewa shirya boren aka yi kuma tsara shi daga Amurka, yana mai zargin Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton.
A wajensa, Putin na ganin an saka ɗambar fafatawa saboda ƙasashen Yamma na shirin ganin bayansa.
Killace kai daga annobar korona a 2020 zuwa 2021
Lokacin da annobar korona ta karaɗe duniya, Putin ya killace kan sa ta hanyar da ba a saba gani ba ga shugabanni masu iko irinsa.
Duk wanda zai gana da shi sai ya killace kansa tsawon mako biyu kuma ƙarƙashin sa idon jami'an tsaro, sannan ya bi ta ƙarƙashin hasken da ke wanke mutum daga ƙwayoyin cuta.
A wannan lokacin, adadi mai yawa na abokansa da masu ba shi shawara sun gaza ganin sa, sai 'yan kaɗan da ke yi masa biyayya ƙwarai da gaske.
Bayan ya killace kan sa daga ganin mutane da yawa da kuma shawarwarinsu, Putin ya yi zaton cewa dukkan abin da yake tunani daidai ne, kuma aka dasa tsiron mamayeUkraine.











