Portugal ta musanta Ronaldo ya yi barazar barin sansaninta a Qatar

An wallafa

Hukumar kwallon kafar Portugal ta musanta cewar Cristiano Ronaldo ya yi barazanar zai bar sansaninta a Qatar.

Wasu rahotanni daga Portugal sun ce kyaftin din mai shekara 37 ya yi barazar barin Qatar, bayan da ya san ba za a saka shi a karawar zagaye na biyu da Switzerland ba.

A wasan da Portugal ta kara da Koriya ta Kudu, Ronaldo ya nuna fushinsa da aka sauya shi a fafatawar a Gasar Cin Kofin Duniya.

Hukumar kwallon kafar Portugal ta ce '' Cristiano Ronaldo bai yi barazanar barin sansaninta ba.''

Ronaldo da Manchester United sun raba gari a tsakaninsu tun kan fara Gasar Kofin Duniya, bayan wata hira da ya yi da Talk Tv.

A hirar ya ce an yaudare shi a United, kuma baya martaba koci, Erik ten Hag.

An canja Ronaldo a wasan farko a cikin rukuni, kuma koci Fernando Santos ya ce ''Bana son yadda Ronaldo ke nuna bacin rai da aka sauya shi a fafatawa da Koriya.''

A wasan Portugal da Switzerland ta fara da Goncalo Ramaos, wanda ya maye gurbin Ronaldo, kuma ya ci kwallo uku a nasarar 6-1 da ta yi.

Ronaldo wanda ya yi wa Portugal wasa 195 da ci mata kwallo 118, bai da yarjejeniya da wata kungiya kawo yanzu, amma an ce wata kungiya a Saudi Arabia ta yi masa tayi mai tsoka.

Portugal za ta kara da Morocco ranar Asabar a wasan daf da na kusa da na karshe.