Man City da Chelsea sun raba maki a Premier

An wallafa

Manchester City da Chelsea sun tashi 1-1 a wasan mako na 25 a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a Ettihad.

Chelsea ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Raheem Sterling a minti na 42, kuma haka suka je hutu ƙungiyar Stamford Bridge ta ci 1-0.

Sterling ya zama na farko da ya ci City gida da waje a Premier League, kungiyar da ya baro ya koma Chelsea da taka leda.

Aguero ne kan gaba a cin ƙwallaye a Etihad a Premier League mai 106, sai kuma Sterling na biyu mai 52 a raga.

Daga baya ne City ta farke ta hannun, Rodrigo Hernandez saura minti bakwai a tashi daga karawar.

Kungiyoyin biyu sun kara a bana a Premier League cikin watan Nuwamba, inda suka tashi 4-4 a Stamford Bridge.

Da wannan sakamakon City ta koma ta ukun teburi da maki 53, mai kwantan wasa daya.

Ita kuwa Chelsea tana ta 10 da maki 35, bayan fafatawar mako na 25.

Ranar Talata 20 ga watan Fabrairu City za ta buga kwantan wasan mako na 18, inda za ta karbi bakuncin Brentford a Etihad.

Ita kuwa Chelsea za ta buga wasan karshe da Liverpool a League Cup da su fafata ranar 25 ga watan Fabrairu.

Sai dai kafin nan Chelsea za ta karbi bakuncin Tottenham a wasan mako na 26 a Premier League a Stamford Bridge.