Wace ce za ta zo ta daya a Gasar Hikayata ta 2022?

Wace ce za ta zo ta daya a Gasar Hikayata ta 2022?
An wallafa

Mutum uku da ke gaba-gaba a Gasar Hikayata ta 2022 sun bayyana fatansu kan gasar, sa'o'i kafin a bayyana wacce ta yi nasara.

A cikin wannan bidiyon duk matan uku na fata ta zo ta daya.

Labaran guda uku dai su ne 'Haihuwar Guzuma' na Hassana Labaran Ɗanlarabawa daga birnin Kano da ke Najeriya da 'Gudun Gara' na Amira Souley daga birnin Maradi a jamhuriyar Nijar da kuma labarin 'Al’ummata' da Maryam Muhammad Sani ta rubuta daga birnin Kanon Najeriya.

A yau Alhamis (03 ga watan Nuwamban 2022) za a yi gagarumin biki inda za a sanar da labarin da ya zamo na daya da na biyu da kuma na uku.

BBC za ta karrama wadanda suka zamo na daya da biyu da uku din da kudi da shaida da kuma lambar yabo, a karo na bakwai na bikin karrama wadanda labarin nasu ya ciri tuta.