Man United ta lashe FA Cup za ta je Europa League a badi

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta lashe FA Cup na bana, bayan da ta doke Manchester City 2-1 ranar Asabar a Wembley.
Minti 30 ana tsaka da wasa United ta ci ƙwallo ta hannun Alejandro Garnacho, sannan minti tara tsakani ta kara na biyu ta hannun Kobbie Mainoo.
Garnacho ya zama na uku matashin daga Manchester United da ya zura ƙwallo a raga a wasan karshe a FA Cup, bayan Norman Whiteside a fafatawa da Brighton a 1983 da Cristiano Ronaldo a karawa da Millwall a 2004.
Kobbie Mainoo mai shekara 19 da kwana 36 da kuma Alejandro Garnacho mai shekara 19 da kwana 329 sun zama matasan farko da aka fara wasan karshe a FA cup da su, tun bayan ƴan ƙwallon Millwall a 2004.
United, wadda ta kare a mataki na takwas a teburin Premier League a bana ta zama ta farko ta kasa - kasan teburi da ta lashe kofin, bayan Arsenal da itama ta kare ta takwas a 2019/20 karkashin Mikel Arteta.
Ita kuwa Manchester City ta zama ta farko mai rike da kofin da aka doke ta a karawar karshe, bayan Manchester United a 2004/05.
United ta ɗauki fansa a kan abokiyar hamayya City, wadda ta doke ta 2-1 a wasan karshe a bara ta lashe FA Cup na bakwai jimilla.

Asalin hoton, Getty Images
Da wannan sakamakon United, wadda ta kare a mataki na takwas za ta buga Europa League kai tsaye a badi tare da Tottenham, wadda ta yi ta biyar din teburi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ita kuwa Chelsea, wadda ta yi ta shida a teburin Premier League a kakar nan, za ta buga wasan cike gurbin shiga Europa Conference League.
To sai dai Newcastle United wadda ta karkare a mataki na bakwai a teburin Premier League ta rasa gurbin buga Europa Conference League a badi.
Newcastle ta buga Champions League a bana, bayan rabonta da gasar shekara 20, amma ta kasa kai wa zagaye na biyu.
Kungiyoyin da za su wakilci Ingila a badi a Champions League sun hada da hudun farko, wato Manchester City da Arsenal da Liverpool da kuma Aston Villa.
Wadanda za su buga Europa kuwa sun hada da Tottenham da kuma Manchester United, yayin da Chelsea za ta fafata a karawar cike gurbin shiga Europa Conference League a badi.
Da yake za a fara sabuwar gasar zakarun Turai a badi, watakila hukumar ƙwallon kafa ta Turai ta fitar da wasu karin ƙungiyoyin daga Ingila da za su buga wasannin badi.
Wasannin da aka buga a bana tsakanin Man City da Man United:
English FA Cup Asabar 25 ga watan Mayun 2024
- Man City 1 - 2 Man Utd
English Premier League Lahadi 03 ga watan Maris 2024
- Man City 3 - 1 Man Utd
English Premier League Lahadi 29 ga watan Oktoban 2023
- Man Utd 0 - 3 Man City
Jerin ƙungiyoyin da ke kan gaba a yawan lashe FA Cup:

Asalin hoton, Getty Images
- Arsenal 14
- Manchester United 13
- Liverpool 8
- Chelsea 8
- Tottenham 8
- Manchester City 7
- Aston Villa 7
- Newcastle United 6
- Blackburn Rovers FC 6
- FC Everton 5
- West Bromwich Albion 5
- Wanderers 5
- Wolverhampton Wanderers 4
- Bolton Wanderers 4
- Sheffield United 4
- West Ham United 3
- Sheffield Wednesday FC 3
- Portsmouth 2
- AFC Sunderland 2
- Nottingham Forest FC 2
- Preston North End 2
- Bury F.C 2
- Old Etonians F.C 2
- Leicester City 1
- Wigan Athletic 1
- Wimbledon FC 1
- Coventry City 1
- Ipswich Town FC 1
- Southampton 1
- Leeds United 1
- Blackpool FC 1
- Charlton Athletic FC 1
- Derby County FC 1
- Cardiff City 1
- Huddersfield Town 1
- Burnley FC 1
- FC Barnsley 1
- Bradford City FC 1
- Notts County FC 1
- Blackburn Olympic 1
- Old Carthusians F.C 1
- Clapham Rovers F.C 1
- Royal Engineers A.F.C 1
- Oxford University A.F.C 1











