Fitaccen masallacin da aka lalata garin gyara

An wallafa

Jami’ai a Iran sun tabbatar da lalata wani masallaci mai dadadden tarihi tun karni na 17, a lokacin da ake kokarin gyara shi.

 

Ana kallon masallacin Shah da ke Isfahan a matsayin mafi kyawu a daukacin kasar Iran, kuma daya ne daga cikin wuraren Tarihi da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe.

 

Sai dai hotunann baya-bayan nan na masallacin sun nuna yadda wani bangare na masallacin ya karkace, yayin da zanen furannin da aka yi amfani da su domin kawata bangon masallacin sam ba su dace ba.

 

Jami’ai sun amince da hakan, sun kuma dauki alkawarin gyarawa, a cewarsu aikin sake gyaran masallacin bai kammalu ba kamar yadda Mehdi Pakdel ya bayyana.

 

Mr Pakdel, ya dora alhakin wannan kuskure kan karafan da aka yi amfani da su wajen isa saman ginin masallacin, har zuwa Hasumiyar mai nisan mita 54.

 

An yi amannar cewa an gina masallacin ne a lokacin da birnin Isfahan, na uku mafi girma a Iran ke kan ganinyar daukar hankalin baki masu yawon bude ido.

 

Launin sararin samaniya da kwaiduwar kwai da aka yi amfani da su wajen shimfida tayal din masallacin, wanda ‘yan Iran da Musulmai wadanda ke zuwa ziyara da shiga ciki domin yin sallah na daga cikin abin daukar hankali a wajen.

 

"Wadanda ke kula da masallacin da masu sa ido ne suka lura akwai matsaloli a ginin musamnman ma dai can saman hasumiyar," in ji Alireza Izadi, shugaban da ke sa ido kan wuraren tarihi a kasar kamar yadda kafar yada labaran Iran ta bayyana.