Matashin da ya ƙirƙiri manhajar ‘Unlock Arewa’

Matashin da ya ƙirƙiri manhajar ‘Unlock Arewa’
An wallafa

Nasir Bappi, matashin nan da ya samar da manhajar 'Unlock Arewa' a yanar gizo ya ce ya iƙiri manhajar ne don nuna wa duniya kyayawan al'adun Hausawa na gargajiya.

Matashin wanda ƙwarrene a fannin fasohohin zamani ya ce ya buɗe manhajar ne don sauƙaƙa wa mutane wajen musayar fasahohi tare da haɓaka kasuwanci tsakanin juna.

Nasir Bappi haifafen jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ce manhajar za ta taimaka wajen yaɗa kyawawan al'adu da ɗabi'un Hausawa a faɗin duniya.

Manhajar ta ƙunshi al'adun Hausawa da dama ciki har da abinda ya shafi masarautu, da sutura da abinci da sauran abubuwan al'adar Malam Bahaushe.

Sabuwar manhajar na ɗauke da al'adun garuruwan Hausawa daban-daban da ire-iren abincin da aka fi ci a waɗannan garuruwa.

Ya ce babban burinsa shi ne taimaka wa mutane domin taimaka wa mutane wajen yaɗa kasuwancisu ta hanyar manhajar