Daga Bakin Mai Ita tare da Nura M Inuwa
An wallafa
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon...
Daga Bakin Mai Ita shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsu zalla.
A wannan kashi na 106, mun tattauna da fitaccen mawaki a masana'antar Kannywood da kuma kasashen Hausa Nura M Inuwa.
Nura ya amsa tambayoyi da dama kan rayuwarsa, musamman watsa masa asid da wasu mutane suka yi a baya, da yadda ya soma waka da kuma nasarori da ya samu a rayuwarsa.
Mawakin ya kuma fada mana bakandamiya cikin wakokinsa masu dumbin yawa da ya rera.