Bidiyon jana'izar Sani Dangote ƙanin Aliko
An wallafa
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
A ranar Laraba ne aka yi jana’izar Alhaji Sani Dangote kani ga Alhaji Aliko Dangote a birnin Kano da ke Najeriya.
Alhaji Sani Gote ya rasu ne a kasar Amurka ranar Lahadi bayan shafe shekaru hudu yana fama da rashin lafiya, kuma an kawo gawar tasa da asubahin yau.
Daruruwan mutane ne suka halarci jana’izar mamacin da aka gudanar a fadar Sarkin Kano.