Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yemen: An kai harin makami mai linzami makarantar Islamiyya
Akalla farar hula 29 ne suka mutu wasu gwammai suka ji munanan runuka a arewacin Yemen, lokacin da 'yan tawayen Houthi suka kai harin makami mai linzami a wata makarantar Islamiyya da masallaci.
Hukumomi sun ce mata da kananan yara na daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda ke fakewa a makarantar sakamakon rasa muhallansu, a harin da aka kai da daddare a gundumar Marib.
'Yan tawayen Houthi ba su ce uffan kan harin ba, wadanda suka zafafa kai hare-hare da karbe iko da Marib a wannan shekarar.
Yankin mai arzikin man fetur shi kadai ya rage a arewacin kasar da gwamnatin Yemen ke tutiya da shi tun bayan fara yakin basasar kasar shekaru shida da suka gabata.
Kuma sama da mutum 100,000 suka mutu, wasu miliyoyi na fama da matsananciyar yunwa sakamakon rashin abinci , da Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla farar hula miliyan 20 ke tsananin bukatar agaji.
Ministan yada labaran Yemen Moammar al-Eryani, ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa 'yan tawayen Houthi da Iran ke mara wa baya, sun yi nufin kai harin ne gundumar al-Jawa mai nisan kilomita 50 daga kudancin birnin Marib, inda suke amfani da manyn makamai masu cin dogon zango mallakar kasar Iran.
Ko a baya an kai wasu hare-hare yankin da ke kusa da al-Amoud, mai cike da hada-hadar mutane kuma mazaunin yawancin 'yan gudun hijira da suka rasa muhallansu ke samun fakewa.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda jini ya malale wata darduma, da littafai a cikin makarantar.
Daga bisani gidan talbijin al-Arabiya na Saudiyya, ya rawaito cewa an zakulo gawawwakin mutum 39 daga baraguzan gini, sai dai kawo yanzu gwamnati ba ta tabbatar da hakan ba.
Ministan yada labarai Mista Eryani, ya yi alla-wadai da harin tare da kira ga kasashen duniya da suka yi gum da bakinsu, su fito domin barawa da daukar mataki kan abin da ya kira kisan kare dangin da 'yan tawayen Houthi ke yi wa farar hula a kasar ta Yemen.
A ranar Alhamis din makon jiya, wasu kananan yara na daga cikin mutum 12 da harin makami mai linzamin da 'yan Houthi suka kai ya hallaka, a yankin da magoya bayan gwamnati da ke zaune a al-Jawba suke.
Rikici tsakanin gwamnatin Yemen da yan tawayen Houthi ya kara munana a shekarar nan, bayan 'yan tawayen sun karbe iko da yawancin yammacin kasar, tare da tilasta wa Shugaba Abdorrabou Mansur Hadi tserewa daga kasar lamarin da ya janyo kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin zafafa kai nasu hare-haren.