Maulidi: Yadda aka gudanar da bikin a birnin Kumasi na Ghana
Latsa hoton bidiyon don ganin yadda aka gudanar da bikin Maulidi a birnin Kumasi na Ghana.
Rabiul Awwal, wata ne na kalandar musulunci da wani bangaren musulmin duniya ke bikin zagayowar ranar da aka haifi manzon Allah, Annabi Muhammad S.A.W.
Musulmai da dama sun yi amannar cewa a watan Rabiu'l Awwal, aka haifi Annabi Muhammadu (SAW).
Sai dai ba dukkanin Musulmi ne ke bikin haihuwar Ma'aiki SAW, saboda sabanin fahimta. Akwai wani ɓangare na malamai da ke nuna rashin dacewar gudanar da bikin maulidi.
Amma wani ɓangare na malamai na kwadaituwa da maulidi suna masu cewa al'ummar Musulmai za su iya yin dukkan abin da suke gani Allah da Manzonsa sun yarda a yi, sai su yi domin nuna murnarsu.
A wannan shekarar ba a bar Musulmi Ghana a baya ba, inda aka gudanar da wani gagarumin maulidi na makarantar wataniyya da ke birnin kumasi a yankin Ashanti.
Wannan shi ne karo na 77 da ake gudanar da irin wannan taro a wannan makaranta.