Muhammadu Buhari: Yadda ƴan Borno ke shirin tarbar shugaba Najeriya
An wallafa
Latsa sama domin kallon bidiyon yadda ƴan Borno ke shirin tarban shugaba Buhari
Borno ce jihar da ta zama hedikwatar ƙungiyar Boko Haram inda ake fama da hare-haren mayaƙan.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya roƙi ƴan jihar da su ba da goyon baya da fatan alheri a yayin ziyarar.
"Ina sake gode muku kan goyon bayan da kuka bai wa gwamnatin nan. Ina godiya bga kowa da kowa, kan goyon bayanku da fatan alherinku da addu'o'i da kuma zamantowarku ƴan ƙasa na gari," kamar yadda sanarwar ta ce.
Lokaci na ƙarshe da Shugaba Buhari ya kai ziyara Borno shi ne ranar 12 ga watan Fabrairun 2020, inda har wani dandazon mutane suka yi wa shugaban ihun ''ba ma yi, ba ma yi''.