Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shafukan sada zumunta ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwar matasa
Yawan amfani da shafukan sada zumunta na matuƙar shafar lafiyar ƙwaƙwalwar matasa, a cewar wani rahoto.
Rahoton ya gano cewar da zarar yara maza da mata sun kai shekara 14, lafiyar ƙwaƙwalwarsu kan fuskanci koma baya.
Rashin motsa jiki na ɗaya daga cikin abubuwan da ke janyo haka - amma kuma annobar korona ta ƙara dagula lamarin, a cewar rahoton.
Bincike ya nuna:
Yarinyar mace ɗaya cikin uku ba ta farin ciki da kamanninta a lokacin da za ta kai shekara 14.
Adadin matasa da ke fama da matsalar ƙwaƙwalwa ya ƙaru sosai.
Ƙoshin lafiyar ƙwaƙwalwar duka jinsin na raguwa a shekarun balaga inda aka fi ganin hakan a mata a cewar rahoton.
Sai dai kuma ya gano da zarar yara mata sun haura waɗannan shekarun, ƙoshin lafiyar ƙwaƙwalwarsu na ƙaruwa sannan ya daidaita yayin da na maza ke ƙara yin ƙasa.
'Ɗebe kewa'
An alaƙanta yawan amfani da shafukan sada zumunta da matsalar ƙwaƙwalwa da yin ɗar-ɗar, inda mata matasa suka fi shiga halin tsananin damuwa da cire tsammani da rayuwa.
"Waɗanda ke fama da wata matsala ta ƙwaƙwalwa kan riƙa shiga shafukan sada zumunta don samun kwanciyar hankali ko kuma don su ɗebe kewa," in ji Dokta Amy Orben wata mai bincike a Jami'ar Cambridge.
Binciken ya yi amfani da bayanan matasa 5,000 a Ingila.
Sannan an sake yin wani bincikena a watan Nuwamba don duba yadda annobar korona ta shafi mutane.
Binciken ya gano cewa matsayin iyalin, wato ko talauci ko arziƙi, da idan ana yawan motsa jiki da rashin lafiyar uwa na cikin abubuwan da suka taimaka wajen taɓarɓarewar lafiyar ƙwaƙwalwar matasa.
Amma yawan motsa jiki na taimakawa sosai ga duka jinsin musamman wurin gyara lafiyar ƙwaƙwalwarsu.
"Saboda kullen korona da aka shiga, makarantu sun rufe don haka matasa ba sa samun damar yin wasannin motsa jiki. Wannan ya ƙara janyo taɓarɓarewar lafiyar ƙwaƙalwarsu," a cewar rahoton.
Rahoton ya bayar da shawarwari kamar haka:
- A riƙa koya wa matasa yadda za su kula da kansu
- Ya kamata a samar wa matasa hanyoyin da za su samu tallafi game da cutukan ƙwaƙwalwa da motsa jiki.
"Wannan da siratsin na tsakanin yarinta da shekarun balaga na da wahala, kuma wanann rahoton ya gano dalilin da ya sa tallafawa matasa ke da matuƙar amfani, bugu da ƙari ga tasirin wannan annoba," a cewar Jonathan Townsend, Shugaban Gidauniyar The Prince da ke Burtaniya.
"Annobar nan ta shafi matasa fiye da kowa, don haka yana da muhimmacin yanzu fiye da ko wane lokaci su samu goyon baya a ɓangaren lafiyar ƙwaƙwalwa."