Habasha ta hana 'yan tawayen Tigray guduwa Sudan

Dakarun gwamnatin Habasha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dakarun gwamnatin Habasha
An wallafa

Habasha ta tura dakarunta zuwa kan iyakarta da Sudan a wani yunkuri na han 'yan kasar tsallakawa domin gudun yakin da ake yi a yankin Tigray na arewacin kasar.

Yankin na tsakiyar wani yakin basasa ne tsakanin gwamnatin tarayyar kasar da dakarun jam'iyya mai mulkin yankin Tigray mai suna Tigray People Liberation Front,TPLF.

Saboda rashin sahihan bayanai daga yankin na Tigray, ana fargabar halin da fararen hula ke ciki.

A halin da ake ciki, gwamnatin ta Habasha ta ce za ta yi yunkurin kutsawa cikin babban birnin kasar Mekelle bayan da wa'adin da aka dibar wa mayakan 'yan Tigray su mika kansu ke daf da wucewa.

Bayanan bidiyo, Ethiopia: Kalli lokacin aka kai mummunan hari babban birnin Tigray a Habasha

Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Sudan ta ce suna karbar kimanin 'yan gudun hijira 1,200 ne a kowace rana.

Amma wakiliyar BBC da ke kan iyakar ta ce a wannan yinin ba ta ga dan gudun hijira ko guda ba, kuma ta ce ta ga kimanin sojoji 12 a bangaren kan iyakar kasar ta Habasha.

Ta ce 'yan gudun hijra sun tabbatar ma ta cewa sojojin gwanatin tarayya ne, kuma sun rika hana 'yan yankin Tigray din tsallakawa cikin Sudan.

Yawancin 'yan gudun hijirar da suka tsallaka kafin a fara wannan hanin na bayyana damuwarsu kan danginsu da ke cikin yankin da masu nazari ke cewa yakin da ake yi zai kara kazancewa ne.