Pence da Kamala sun kara kan annobar korona da haraji a muhawararsu

An wallafa

Mataimakin shugaban AMurka Mike Pence da 'yar takarar mukamin mataimakin kasa ta jam'iyyar Democrat, Kamala Harris sun kara kan annobar barnar da korona ta yi a Amurka.

Sanata Kamala ta tuhumi MIsta Trump da abin da ta kira "gazawa mafi girma da muni ta dukkan gwamnatocin Amurka cikin tarihin kasarmu."

Mista Pence ya ze 'yan takarar jam'iyyar Democrat ba su da wani shiri da ya wuce kwafan abin da gwamnatinsu ke yi a yanzu.

Mista Biden na gaba da Mista Trump a ra'ayin jama'a da aka dauka ana saura kwana 27 a gudanar da babban zaben kasar.

Ba kamar yadda waccan muhawarar tsakanin shugaba Trump da Joe Biden ta gudana ba, a wannan karon - yawanci 'yan takarar biyu sun mutunta tsarin da aka shirya.

An dai raba Kamala Harris ta jam'iyyar Democrat da Mike pence na jam'iyyar Republican da wani gilashi mai kauri domin kiyaye yaɗa cutar korona, amma duk da haka akwai lokutan da suka kara da kalamai masu zafi.

Yawancin batutuwan da suka tattauna a kai sun fi shafar annobar korona ne, inda Sanata Kamala ta yi watsi da yadda Mista Trump da mataimakin nasa Mike Pence suka gudanar da shirin kare Amurkawa daga annobar.

Kamala Harris ta ce "Amurkawa shaidu ne ga gazawa mafi muni da wata gwamnatin kasar nan ta taba yi cikin tarihin kasarmu. Ga kuma gaskiyar lamarin; Mutum 210,000 sun mutu a kasar nan cikin watanni kalilan.

''Mutum fiye da miliyan bakwai sun kamu da cutar korona. An rufe kashi daya bisa biyar na dukkan kamfanonin Amurka. Muna kuma kallo yadda mutum fiye da miliyan talatin suka rasa ayyukan yi."

Ta kuma ce "Tun ranar 28 ga watan Janairu aka sanar da mataimakin shugaba Pence da mai gidansa game da hatsarin wannan cutar.

''Amma sai suka ki sanar da ku. Sai suka boye bayanan daga gareku. Amma abu mafi takaici shi ne har yau da nake muku maganar nan, ba su da wani shirin magance matsalar da annobar ta haifar."

A martanin da ya mayar, mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya soki Sanata Kamala da yi wa Amurkawa zagon kasa idan aka samar da rigakafin cutar ta korona.

"Gaskiyar lamarin sanata, shi ne muna daf da samar da rigakafi cikin lokaci ƙanƙani, kasa da shekara guda. Muna da kamfanoni biyar da suka yi nisa wajen gwaje-gwajen rigakafi a halin yanzu, kuma muna kan aikin samar da miliyoyin allurar rigakafin.

''Saboda ahaka nake ganin ba ki da hurumin karya wa jam'a karfin gwuiwa kan kokarin da gwamnatinmu ke yi na samar da riga-kafi."

Mista Pence dai ya kaucewa amsa tambayoyi kan ko sun tattauna da shugaba Trump kan ko zai gaje shi idan rashin lafiyar shugaban ta tsananta.