Sudan : An rattaba hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya a kasar

An wallafa

An cimma wata muhimmiyar yarjejeniya game da kokarin samar da dawwamammen zaman lafiya a Sudan, wadda aka sa wa hannu a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu.

Bikin sa hannu a yarjejeniyar ya samu halartar shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kirr da dubban jama'ar kasashen biyu.

Hakan dai ya biyo bayan tattaunawar da aka kwashe watanni ana yi, wadda Sudan ta Kudu ta jagoranta

An yi ta rafka shewa da murnar samun wannan gagarumar nasara, yayin da wasu ke daga tutoci sama.

Dubban mutane ne, wadanda suka hada da wakilai daga dukkan fadin kasar, suka yi ta maza, suka hallara wajen bikin sa hannun, da aka gudanar a filin wasan kwallon kafa da ke Juba, babban birni Sudan ta Kudu. Duk kuwa da makeken ruwan saman da aka yi ta tafkawa.

Yarjejeniyar ta karshe da aka sa wa hannu a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoban, 2020, tsakanin bangaren gwamnatin rikon kwarya da na 'yan tawayen Sudan Revolutionary Front, a hukumance ta kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru goma sha bakwai ana yi, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka masu dumbin yawa, ya kuma kai ga bude hanyar kafa gwamnatin farar hula.

Yarjejeniyar dai ta fi mayar da hankali ne ga batun tsaro da hakkin mallakar filaye, da rabon mukamai, da kuma sake tsugunnar da mutanen da suka rasa muhallansu.

Sai dai kuma duk da cewa gamayyar kungiyoyin 'yan tawaye daban-daban, daga yankunan kasar da dama ne suka hallara wajen sa hannu a yarjejejniyar, akwai wasu kungiyoyin tawaye biyu da ba su shiga yarjejeniyar ba.

Wasu dai na ganin cewa tsohon shugaban kasar Omar Al Bashir, ya gudanar da mulkinsa ne da rashin sassauci, musamman ta fuskar kama 'yan adawa da hana jama'a walawa.

Amma kuma bayan jerin zanga-zanga da masu rajin kafa tsarin dimokradiyya suka yi ta yi daga karshe an hambarar da gwamnatinsa a 2019, kuma a halin yanzu wata kotu tana yi masa shari'a.

Ita dai gwamnatin rikon kwaryar ta Sudan, ta bayar da karfi ne ga kokarin warware rikice-rikicen cikin gida, da kuma sake gina tattalin arzikin kasar.