Sani Abacha: 'Sau takwas aka yi yunkurin yi masa juyin mulki – Hamza Al-Mustapha

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon babban dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya ce sau takwas ana yunkurin yi wa tsohon shugaban kasar juyin mulki.
"Kafin lokacin da ya rasu, ana shirin yi masa juyin mulki na takwas ne amma 'yan Najeriya su iya sannsu shi ne an yi masa yunkurin juyin mulki na uku ne amma gaskiyar magana ita ce guda takwas ne aka yi, a kan na takwas din ne ya rasu," in ji Al-Mustapha a hirarsa da BBC a dai-dai lokacin da marigayi Abacha ya cika shekara 22 da rasuwa.
Al-Mustapha ya ce akwai gyara daga rahotannin da ake zargin cewa kudin da ake mayar da su Najeriya na tsohon shugaban ne.
Ya ce wadannan kudade mallakar gwamnatin Najeriya da shugabannin al'ummar kasar su ka amince a ajiye su a asusun kasashen waje ne.
A cewarsa, "Akwai lokacin da za a sakawa Najeriya takunkumi mai zafi, akwai shiri da aka yi na ajiye kudi a waje saboda koda an sa takunkumin ba zai bar Najeriya da 'yan Najeriya su tagayyara ba."
Ya ce "Na san an yi taro har da sarakuna na kudu da na arewa da manya-manyan wanda aka sani na kasar, da wanda suke cikin mulki da wanda suke wajen mulkin, aka tafi wani wuri cikin 'Brigade of Guards' ana kiran shi 'Officers' Mess' a nan aka yi wannan taro.
"Aka yi bayanin mene ne wannan takunkumi da za a sa kuma suka yanke shawarwari, to daga nan ne aka je aka ajiye wadannan kudade, wannan akwai (ma'aikatar) kudi, akwai bankin kasa, akwai sakataren gwamnati, akwai (ma'aikatar) tsare-tsare."
Manjo Al Mustapha ya ce ya yi mamaki yadda ake danganta kudaden da Abacha saboda "idan za ka bude (asusu) na kudi da sunan wane, shi wannan wanen ne zai je ya saka kudi a wannan kasar wajen, sai ya saka hannu, sai an dauke shi a hoto, sai an nuna dalilai da inda kudin yake zuwa,"
A cewarsa, fito da wadannan bayanai ne kadai zai iya tabbatar da ko wadannan kudaden suna da alaka da Abacha ko kuma a a ganin cewa "shi da bai taba zuwa kasar da ake dauko wadannan kudaden ba, ya aka yi aka sa kudi, ya aka yi (asusu) ya zama nasa,"
"Tun da aka kama ni ai nima na musu tambayoyi da yawa, ina saka hannun shi marigayi Abacha a takardun, ko ya dangwala hannu da sunan nasa ne, toh sai ku nunawa duniya."
Sai dai Al Mustapha ya ce a lokacin da Abacha ya hau mulki, kudin da yake waje na Najeriya bai kai dala miliyan 200 ba, "tsaro ya tabarbare, a cikin shekara hudu da wata bakwai ya yi duk yadda ya yi aka tarawa kasar waje dala biliyan tara da miliyan dari bakwai da talatin da biyu."
"Amma bayan ya rasu a cikin wata tara, wannan duk biliyoyin da aka tara sun bata, amma shi Abacha da ya tara kudin ya dawo da martabar Najeriya aka gyara tsaro, shi ake zagi,"
"Kuma wanda suka yi wawason wannan kudin da ya tara na shekara hudu suna nan da rai ba wanda ya taba su, da shi ma yana da rai, ba mai taba shi a yau," kamar yadda Al Mustapha ya bayyana.










