Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: WHO ta yabi Saudiyya saboda hana zuwa Umra
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yaba wa Saudiyya saboda hana zuwa Umra kasar domin dakile yaduwar cutar COVID-19, wato coronavirus.
Ofishin WHO na Gabashin Mediterranean ya ce matakin zai hana taruwar mutane da kuma yiwuwar yaduwar cutar a lokacin Umra ko ziyara.
''Hana shigowar miliyoyin maniyyata Umra da masu ziyara daga kasashe zai saukaka wa Saudiyya aikin hana shigar cutar da yaduwarta a kasar,'' a cewar hukumar.
Gwamnatin Saudiyya ta hana shiga kasarta domin yin Umra ko ziyara ko yawon bude ido saboda cutar da ta kashe dubban mutane a duniya.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta ce kasar na lura da yanayin da duniya ke ciki game da coronavirus tare da daukan matakan hana shigarta kasar ko yaduwarta.
Baya ga mace-mace, annobar COVID-19 ta kwantar da dubban mutane tare da tilasta killace wasu garuruwa da makarantu da tarukan al'umma a wasu kasashe.
Sauran matakan da kasashe suka dauka na hana yaduwar COVID-19 sun hada da killace wadanda suka shigo daga kasashen da aka samu bullar cutar na tsawon kwana 14.
COVID-19 a kasashe
WHO ta ce barkewar cutar na karuwa, inda ta gargadi kasashen duniya su kasance cikin shirin ko ta kwana kan barkewar cutar, da ta yadu zuwa kasashe fiye da 50.
Hukumar ta nuna matukar damuwa game da yaduwar cutar a Iran, inda mataimakiyar shugaban kasar da wasu manyan jami'an gwamnati suka kamu da cutar.
Za a tura wata tawaga a makon gobe, yayin da hukumomin Iran ke shirin rufe makarantu na tsawon kwana uku a kasar.
Jamus da Switzerland su ne kasashe na baya-bayan nan da suka bayyana karin daukar matakai na dakile yaduwar cutar.
Amma har yanzu Korea ta Kudu ce ta fi yawan masu kamuwa da cutar kowace rana.
Najeriya da Mexico sun bayyana bullar cutar a kasashen su.
COVID-19 a Najeriya
Bullar coronavirus a Najeriya shi ne karon farko da aka tabbatar da bullarta a yankin Yamma da Saharar Afrika.
Ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya ce ba a gano cutar ta farko a kasar ba a lokacin da mutumin da ya kai ta kasar ya sauka a filin jirgin sama a Legas.
Hukumomi sun ce babu alamun rashin lafiya a tare da mutumin dan kasar Italiya a lokacin da ya isa Najeriya.
Mista Ehanire ya ce za a tuntubi duk mutanen da ke cikin jirgin da mutumin ya hau tare da sanya ido sosai a kan su.
'Mun fara aikin gano duk mutanen da mutumin ya yi mu'amala da su tun daga lokacin da ya shigo Najeriya har ma da wadanda suka shigo kasar tare,'' a cewar ministan.