Wani kulob a Masar ya sayi dan kwallo mai shekara 75

Eez Eldin Bahder

Asalin hoton, Egyptian Football Association

An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Masar (EFA) ta sanar da yi wa dan wasa mafi tsufa a duniya rijista.

Wani kulob din kasar mai suna 6th October ne ya sayi dattijon mai suna Eez Eldin Bahder, duk da bai taba buga kwallo a wata kungiyar a matsayin kwararren dan wasa ba, hasali ma babu wanda ya san shi a harkar tamaula a kasar.

Ba'a bayar da wani cikakken bayani game da sharadin yarjejeniyar ba da ma wa'adin da za ta dauka.

Hukumar kwallon kafar da kuma Eez Eldin Bahder sun gayyaci wakilai daga kundin adana ababen tarihi na duniya domin su shaida wasan farko da dan wasan zai buga domin watsa shi a duniya.

Eez Eldin Bahder

Asalin hoton, Egyptian Football Association