Qasem Soleimani: Mutum 50 sun mutu a turmutsutsun binne shi

Bayanan bidiyo, Mutum 50 sun mutu a turmutsutsun binne Soleimani
An wallafa

Akalla mutum 50 ne suka mutu a wani turmutsutsu a Iran yayin da 'yan kasar ke tururuwa zuwa wajen jana'izar babban kwamandan kasar Qasem Soleimani wanda Amurka ta kashe a makon jiya.

Rahotanni sun bayyana cewa kusan mutum 200 ne suka jikkata.

An rufe marigayin ne a birnin Kerman, inda aka yi kiyasin miliyoyin mutane sun taru a wurin jana'izarsa.

Kashe shi da aka yi ya janyo fargabar yaki tsakanin Amurka da Iran.

Kafin rasuwarsa, ana ganin cewa shi ne na biyu a wurin karfin iko a kasar Iran bayan Jagoran Addinin kasar Ayatollah Ali Khamenei.

Amurka dai na kallon Soleimani a matsayin ''dan ta'adda'' kuma barazana ga sojojin Amurka.