Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kori malaman jami'ar Abuja kan zargin lalata da daliba
Bayanai sun nuna cewa hukumar gudanarwar Jami'ar ce ta amince da korar malaman biyu bayan nazari kan rahoton da kwamitin da ta kafa na mutun takwas ya fitar.
Jami'in hulda da jama'a na jami'ar Dr Habib Yakoob, ya ce an sallami Farfesa Adeniji Adebayo na sashen koyar da aikin gona da Farfesa Agaptus Chibuzo Orji na sashen koyar da kimiyar muhalli.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin daya daga cikin malaman Farfesa Adeniji Adebayo amma bai amsa waya ba, bai kuma amsa gajeren sakon da a ka aika masa ba.
Ko a watan Oktoba ma sashen BBC da ke binciken kwakwaf na (Africa Eye) ya fallasa yadda wasu malaman jami'ar ke neman ci da gumin dalibansu mata, ta hanyar lalata da su don ba su makin jarrabawa a wasu jami'o'in Najeriya da Ghana.
A kan haka ne ma hukumomi a Najeriyar ke yunkurin fito da wata doka da za ta hukunta masu irin wadannan laifuka.