Mauricio Pochettino: Na yi iya bakin kokarina a Tottenham

Pochettino ya samu kashi 55.9% na nasarar da ya samarwa Spurs

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Pochettino ya samu kashi 55.9% na nasarar da ya samarwa Spurs
An wallafa

Tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce ya bayar da gudun mowar da ya kamata ya bayar lokacin da yake kungiyar.

Pochettino mai shekara 47 dan kasar Argentina ya jagoranci Spurs har tsawon shekara biyar da rabi, inda ya kai ta zagaye na karshe a gasar Zakarun Turai.

An maye gurbinsa da Jose Mourinho a makon jiya.

Karon farko kenan da tsohon kocin yayi magana tun bayan da kungiyar ta sallame shi.

"Har ila yau, akwai matsaloli masu yawa kamar yadda ake hangen nasarori," inji Pochettino

"Fatan alheri, na tabbata zamu sake haduwa a nan gaba."

Tsohon dan wasan baya na Argentina Pochettino, wanda kuma ya jagoranci Espanyol da Southampton, ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar a watan Mayun 2018.

Pochettino ya yi wani jawabi a watan Janairun 2019 game da fatan cigaba da kasancewa tare da Tottenham na tsawon shekaru 20.

Spurs ta koma sabon filin wasanta mai dauke da wurin zaman 'yan kallo 62,062 a watan Afrilu bayan kusan shekaru biyu tana buga wasanta na gida a Wembley, amma sun yi kokarin samun daidaito a wannan karon inda ta kasance na 14 a teburi kafin a kori Pochettino.

Pochettino ya kara da cewa "Na yi iya bakin kokarina, musamman abinda aka bukaci nayi tun farko kuma shi na aiwatar".

"Na kuma godewa abokan aikina a Tottenham, da sauran ma'aikatan kulob din da kuma 'yan wasanta sakamakon irin zaman da na yi da su.