Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kashe 'yan bindiga masu safara da bautar da mata a Burkina Faso
Sojoji a Burkina Faso sun ce sun kashe 'yan bindiga 32 - wadanda suka kira "yan ta'adda" - wadanda ke tsarewa da bautar da mata domin yin lalata da su a yayin wani samame da suka kai a arewacin kasar.
Samame na farko ya auku ne a dajin Yorsala inda rundunar sojojin kasar ta ce ta kashe 'yan bindiga 24, amma soja daya ya rasa ransa, a gumurzun da aka shafe sa'o'i ana yi.
Sojojin sun kuma ce sun kashe wasu 'yan bindiga takwas a Bourzanga, kuma sun kwace tarin makamai da kayan yaki.
Masu tayar da kayar baya da ke ikirarin na Musulunci ne na kara kai hare-hare a kasar da ke yankin Afirka ta yamma.
Wadannan samamen na zuwa ne kasa da wata guda da aka kashe wasu ma'aikata 40 na wani kamfanin da ke ayyukan hakar ma'adinai mallakin kasar Canada bayan da aka yi musu kwantan bauna.
Daruurwan mutane su rasa rayukansu, kuma kusan mutum rabin miliyan ne suka tsere daga muhallansu tun da tashin hankalin ya barke a 2015.