Rikicin Kamaru: Iyaye na tsoron kai yara makaranta

Hukumomi a Kamaru sun ba da tabbacin cewa komawa makarantun boko da aka sanya ranar Litinin din na, biyu ga watan Satumba, ba makawa zai tabbata, amma kuma iyaye na dari-dari.
Wasu ministocin kasar ne suka bayyana haka a wata hira da manema labarai game da gargadin da 'yan a-waren yankin renon ingila suka bayar don hana komawa makarantun.
Sanarwar komawa makarantun bokon a ranar ta Litinin a yankin renon Ingila kamar sauran sassan kasar abu ne da ya kasance da mamaki ganin yadda ake tashin-tashina da 'yan a-waren da suka lashi takobin hana hakan.
Amma kuma gwamnati ta kafe cewa lalle ba makawa za a fara karantar da yaran da aka yi wa rijista a kananan makarantu na renon yara da na furamare da kuma na gaba da furamare a duk fadin Kamarun na farkon shekarar karatu ta 2019/2020.

Gwamnatin kasar ta ce fara karatun ya zama wajibi kasancewar ilimi shi ne ginshikin duk wani ci-gaba, amma kuma ta ce sai a nan gaba ne za a sanar da lokacin bude manyan makarantun karatu mai zurfi.
Ta kara da cewa ta kudiri aniyar ganin yara maza da mata a yankunan kudu maso yamma da kuma Arewa maso yamma na kasar sun samu ilimi kamar sauran takwarorinsu na yankin renon Faransa.
Hukumomin Kamarun sun ce sun dauki duk wani mataki na tabbatar da tsaro da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a yankuna renon Ingila da ma sauran sassan kasar don ganin burin samar da ilimin ga al'umma bai samu nakasu ba daga masu tayar da kayar-bayan.
Yayin da hukumomin kasar ke bayar da tabbaci ga iyaye, ana nuna damuwa da shakku kan yadda yara za su iya komawa makaranta har su samu su yi karatu cikin natsuwa yayin da ake cikin hali na rashin tsaro, inda ake kai hare-hare na yaki a yankunan na renon Ingila.
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa kafin a fara rikicin a-waren akwai makarantun yara 5,377 da ake karantarwa a larduna biyu na renon Ingila, amma a yanzu saura makarantu 895 kawai.
Sauran gaba daya 4,482 ko dai sun zama sansanonin masu tayar da kayar-baya ko suna rufe ko kuma sun rushe a sanadiyyar rikicin a-waren.
Kusan a yanzu ana ganin ba wani wuri a kasar da za a iya cewa yara za su zauna su yi karatu cikin kwanciyar hankali, saboda haka tururuwar da a da ake yi ta kai yara makaranta a yanzu abin ya sauya saboda fargabar tsaro.
Duk tabbacin samar da tsaron da gwamnatin Kamarun ke ba wa iyaye na su tura 'ya'yansu makarantun, bai kwanta wa jama'a ba, saboda ba su fasa ficewa daga yankunansu inda suke ganin ba kwanciyar hankali, domin zuwa inda za su iya tsira.
Sai dai a duk rana irin ta yau Litinin, mutane a kusan daukacin yankin suna mutunta dokar k'in fita da masu fafutuka suka sanya.
Baya ga wannan al'amari, 'yan a-waren sun kuma bullo da wata sabuwa, ta durkusar da harkoki tsawon mako 3.










