Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano Pillars ta hau kan teburi, bayan doke Enyimba
Kano Pillars ta yi nasara a kan Enyimba International da ci 2-1 a wasan mako na 25 a gasar Firimiyar Najeriya da suka kara ranar Lahadi a Kaduna.
Enyimba ce ta fara zura kwallo a ragar Pillars ta hannun Victor Mbaoma, kuma haka suka je hutu da ci 1-0.
Bayan da suka koma wasa na biyu bayan hutu kyaftin Rabiu Ali ya farke a bugun fenariti, kuma kwallo na 10 da ya ci a kakar bana kenan.
Kasa da minti 15 a tashi daga wasan Pillars ta kara na biyu ta hannun Ifeanyi Eze da hakan ya bai wa kungiyar Kano maki ukun da take bukata.
Da wannan sakamakon Pillars wadda take bani in baka a jan ragamar teburin Firimiyar Najeriya a bana da Akwa United, yanzu ta koma ta daya a makon nan.
Nasarar da Pillars ta yi a kan Enyimba ta hada maki 48 kenan a karawa 25, ita kuwa Akwa ta tashi 2-2 a gidan Wikki ta samu maki daya kenan ranar Lahadi.
Sakamakon wasannin mako na 25 da aka buga ranar Lahadi:
- Abia Warriors 1 - 1 Ifeanyi Ubah
- Kada City 3 - 0 Jigawa Golden Stars
- Wikki Tourists 2 - 2 Akwa United
- Heartland 2 - 2 Rivers United
- Kano Pillars 2 - 1 Enyimba International
- Adamawa United 0 - 2 Plateau United
- Katsina United 2 - 1 Nasarawa United
- Enugu Rangers International 1 - 1 Mountain Of Fire
- Dakkada 0 - 1 Lobi Stars
- Warri Wolves 2 - 1 Sunshine Stars