Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Damben Dan Aliyu da Shagon Bahagon Kanawa
Dan Aliyu ya buge Shagon Bahagon Kanawa a turmin farko a damben naira dubu dari da suka kara a Dei-Dei da ke Abuja, Najeriya.
Dan Aliyu daga Jamus ya yi nasara ne a kan Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu a turmin farko.
Hakan na nufin Dan Aliyu zai karbi naira dubu hamsin kenan, shi kuwa Shagon Bahagon Kanawa ya karbi naira dubu arba'in ya wanke jikinsa.
Sauran dubu goma a bai wa makada wadanda suka yi wa 'yan damben biyu kida kafin fafatawar a tsakaninsu.
An kuma yi dambe ba kisa tsakanin Bahagon Mai Takawasara Guramada da Bahagon Mancha daga Jamus.
Haka ma fafatawa tsakanin Bahagon Sisco daga Kudu da Shegiyar mota daga Arewa ba wanda ya je kasa.
Damben Hassan Shagon Sojan Kyallu Guramada da Tulan Shagon Tuwa daga Jamus shima bai yi kisa.