Damben Ebola da Bahagon Mai Takwasara a Abuja

An wallafa

Bahagon Mai Takwasara da Ebola sun kara a damben safiyar Lahadi a Dei-Dei da ke Abuja, gidan wasa na Ali Zuma ba kisa.

Kawo yanzu an bari sai da yammaci za a fitar da gwani a tsakaninsu.

Damben mota aka sa musu ga duk wanda ya zama zakara, na biyu ya karbi naira 100,000 domin ya wanke jikinsa.

A bara ne Bahagon Mai Takwasara ya buge Ebola a Dei-Dei a damben Safe.

A makon jiya ne a damben naira 150,000, Bahagon Mai Takawasara ya buge Bahagon Shagon 'Yan Sanda.