Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Garkuwan Musa ya buge Shagon Soja a damben Abuja
An dambata a wasanni da yawa a gidan wasa na Ali Zuma da ke Dei Dei a Abuja Nigeria ranar Lahadi da safe.
Damben da aka yi kisa:
Bahagon Tula ya yi nasara a kan Dan Matawallen Kwarkwada
Shagon Garkuwan Balan Gwambe ya buge Shagon Mustapha
Garkuwan Musan Kaduna ya doke Shagon Sojan Kyallu
Shagon Autan Dan Bunza ya buge Shagon Shagon Mada
Guguwar Mai Takawasara ya yi nasara a kan Autan Bahagon Sisco
Damben da aka yi canjaras:
Shagon Autan Dan Bunza da Autan Shagon Sisco
Aljanin Danladi da Shagon Mu'azu
Autan Ali Zuma da Shagon Autan Dan Bunza
Shagon Dogon Auta da Bahagon Musan Kaduna
Shagon Dan Katsinawa da Malam Malam
Bahagon Alin Tarara da Abba Shagon Sisco
Autan Dan Bunza da Bahagon Bahagon Danm Kanawa