Liverpool ta ci wasa na 21 a Premier bana

An wallafa

Liverpool ta doke Manchester United da ci 2-0 a wasan mako na 23 a gasar Premier da suka kara a Anfield ranar Lahadi.

Liverpool ta ci kwallon farko ta hannun Virgil van Dijk tun kan hutu, daf a tashi daga fafatawar Mohamed Salah ya kara na biyu.

Liverpool ta ci wasa 22 kenan a Premier bana da kunnen doki daya, shi ne wanda ta yi a gidan United a wasan farko da suka kara.

Liverpool mai kwantan wasa daya ta hada maki 64 daga wasa 22, ta kuma bai wa Manchester City ta biyu tazarar maki 16.

A ranar Alhamis Liverpool wadda rabonta da kofin Premier za ta ziyarci Wolverhamption a wasan mako na 24.

Kungiyar ta Anfield ta kafa tarihin bajinta a gasar Lik-Lik ta Turai, bayan buga wasa 22.

A kakar 2017/18 Manchester City ta ci karawa 20, bayan buga gasar Premier da canjaras biyu.

Kungiyar Bayern Munich ce ta fara bajintar yin cin wasa 20 da canjaras biyu a gasar Bundesliga a kakar 2013/14.