Kabakov zai alkalanci wasan Madrid da Brugge

An wallafa

Ranar Talata ne Real Madrid za ta karbi bakuncin wasa na biyu na cikin rukuni a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League.

Real Madrid din za ta fafata ne da Club Bruges a Santiago Bernabeu.

Tuni kuma hukumar kwallon kafar Turai ta bayyana Georgi Kabakov a matsayin wanda zai alkalanci karawar, kuma a karon farko da zai busa wasan Madrid.

Kolakov dan kasar Belgium ya fara aikin alkalancin tamaula a gasar cin kofin Zakarun Turai a wasan mako na shida a bara, tsakanin Valencia da Manchester United.

Haka kuma ya hura wasa shida a gasar Europa League, ciki har da wanda Brugge ta kara a zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a wasannin a kakar 2018/19.

Real Madrid ta yi rashin nasara a wasan farko da ci 3-0 a Champions League a bana a gidan Paris St Germain ranar 18 ga watan Satumba.

Ita kuwa Brugge tashi ta yi babu ci tsakaninta da Galatasaray a dai ranar ta Laraba da Real ta yi wasan ta.

Karawar da za a yi ranar Talata 1 ga watan Oktoba

  • Atalanta da Shakhtar Donetsk
  • Manchester City da Dinamo Zagreb
  • Tottenham da Bayern Munich
  • Tottenham Hotspur Stadium
  • Juventus da Bayer 04 Leverkusen
  • Galatasaray da Paris Saint-Germain
  • Lokomotiv Moscow da Atletico de Madrid
  • Crvena Zvezda da Olympiacos

Fafatawar da za a yi ranar Laraba 2 ga watan Oktoba

  • Genk da Napoli
  • Slavia Prague da Borussia Dortmund
  • Liverpool da Red Bull Salzburg
  • Barcelona da Inter Milan
  • Valencia da Ajax Amsterdam
  • Lille da Chelsea
  • Zenit St. Petersburg da Benfica
  • RB Leipzig da Olympique Lyonnais