Real Madrid vs Osasuna: Zidane ya hutar da Bale

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Zinedine Zidane ya bayyana sunayen 'yan tawagarsa 19 da za su fafata da Osasuna da karfe 8:00 a yau Laraba, sai dai babu Bale a ciki yayin da idonsa daya ke hango karawar Asabar tsakaninsa da Atletico Madrid.

Kocin ba zai samu damar amfani da Ferland Mendy ba da Marcelo da Luka Modric saboda har yanzu suna murmurewa daga raunin da suka ji.

Ba a tsammanin Bale yana fama da kowacce irin matsala kuma Zidane ya zabi Rodrygo Goes a madadinsa, wanda ba a je Sevilla da shi ba a karshen makon da ya gabata.

Shi ma Isco har yanzu bai gama murmurewa ba daga raunin da ya ji a bayan gwiwarsa.

Duk da cewa Marcelo da Mendy suna jinya, abin da ke nuna cewa babu kwararren dan bayan gefen hagu, Zidane ya gwammace ya yi amfani da dan wasan bayan komai-da-ruwanka wato Nacho Fernández.

Wannan karon ma babu Mariano Díaz a tawagar ta Zidane.

Tawagar Real Madrid a wasan na yau:

Masu tsaron raga: Courtois, Areola, Altube.

'Yan baya: Carvajal, Militão, Ramos, Varane, Nacho, Odriozola.

'Yan tsakiya: Kroos, Casemiro, Valverde, James.

'Yan gaba: Hazard, Benzema, Vázquez, Jović, Vinicius, Rodrygo.