Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ranar sikila ta duniya: 'A tabbatar an yi gwajin jini kafin aure'
Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon
A ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin masu fama da cutar amosanin jini wato sikila.
An ware ranar ce domin wayar da kan al'umma muhimmancin kula da masu fama da cutar da kuma taimaka musu.
Albarkacin ranar ta bana, Hajiya Badiyya Magaji Inuwa mai gidauniyar Sickle Cell Patient Health Promotion Centre da ke kula da masu lalurar amosanin jini a Najeriya ta ce abu mafi muhimmanci shi ne mutane su rika yin gwajin jini kafin su yi aure domin hana kamuwa da cutar.
"Da ka ja wa kanka wahala gwamma a rika auna jini, domin da muguwar rawa gwamma kin tashi. Muna rokon mutane su ci gaba da gwaji domin babu dadi ka haifi yaro ya rika shan wahala a duniya," a cewarta.
Hajiya Badiya ta kara da cewa dawainiyar masu sikila akwai matukar wahala, domin samun sauki gwamma mutane su yi gwaji tun farko.
"Hadarin samun da mai sikila yana da wahala, domin ba shi magani da dawainiyar asibiti ma abin tausayi ne".