Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Nau'ukan minshari da matsalolinsa
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Likitoci a fannin bacci sun bayyana cewa akwai nau'in munshari fiye da guda daya, saboda dalilan da ke janyo shi sun sha bamban.
Inda suka bayyana cewa akwai munsharin da kiba ke janyo wa da wanda ya shafi halittar dan adam , sannan akwai na dadin bacci.
Dumbin mutane ne ke fama da matsalar munshari a lokacin da suke bacci, matsalar da ke hana ma'auratansu samun bacci mai inganci.
A cewar likitoci rashin samun isasshen bacci ko katsewa da kasa komawa bacci bayan an farka da matukar gajiya bayan mutum ya kwashe sa'oi yana baccin dare, na daga cikin alamun cewa mutum yana fuskantar cutar rashin bacci.
Cibiyar kiwon lafiya da ke jihar Ohio na Amurka, Cleveland clinic, ta wallafa a shafinta na intanet cewa, mata sun fi maza fuskantar matsalar rashin bacci.
Haka zalika masu ciki da matan da suke samun sauyin wasu sinadarai a jikinsu, gabannin fara jinin al'ada suna cikin rukunin mutanen da ke iya fuskantar matsalar rashin bacci.
Matan da suka daina ganin jinin al'ada, suma akwai yiwuwar su fuskanci matsalar.
Cibiyar ta kara da cewa matsalar rashin bacci ta fi yawa a tsakanin mutanen da suka haura shekara 60 a duniya, saboda sauye-sauyen da suke samu a jikinsu da kuma tsufa.