Gane Mini Hanya: Matsalolin Ilimin Firamare a Najeriya

An wallafa

Danna hoton sama domin sauraren shirin

Batun ilimin firamare wani sha'ani ne da kusan za a iya cewa yana ci wa dukkannin jihohi a Najeriya tuwo a kwarya.

Ma fi yawancin lokuta matsalolin na taimaka wa wajen dakile aniyar iyaye na ganin 'ya'yansu sun yi karatun zamani.

Matsaloli kama daga rashin isassun azuzuwa kuma masu inganci zuwa matsalar karanci da rashin ingancin malamai ne manya-manyan matsalolin da suka zama tamkar sun gagari gwamnatoci.

A cikin wannan shiri na musamman wanda gidauniyar MacArthur ta dau nauyin kawo muku, za mu yi duba kan yanayin makarantu da walwalar malamai, da kuma sauran bukatun fannin ilimi a jihar Adamawa.