Ra'ayi Riga: Matsalar ƙarancin ruwan sha a Kano

An wallafa

Danna hoton da ke sama domin sauraren shirin:

Kano na daya daga cikin birane masu dinbin al'umma a nahiyar Afirka.

A kasashe masu tasowa irin Najeriya, samar da abubuwan bukatu na yau da kullum kan zamo babban kalubale a manyan birane kamar Kano.

Sassa daban-daban na birnin na Kano na ci gaba da fuskantar karancin ruwan sha da na amfanin yau da kullum.

Shin mene ne ya haifar da wannan matsala kuma me ya sa har yanzu hukumomi suka kasa shawo kanta?

Wannan ne abin da aka tattauna a cikin shirin Ra’ayi Riga.