Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Abin da ke janyo zubar jini ga mai ciki
Ku latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:
Mata masu juna biyu za su iya fuskantar zuban jini a yayin da cikinsu yake karami da kuma lokacin da ya fara tsufa.
Likitoci sun bayyana zuban jini idan ciki ya kai kimanin wata bakwai, a matsayin mai hatsari sosai ga uwa da jaririnta.
Kungiyar kwararrun likitoci masu duba lafiya da cututtukan mata ta Amurka, ACOG ta ce mata masu juna biyu 15 zuwa 25 a cikin dari ne ke samun zuban jinni a watanni uku na farko.
Sai dai zuban jini a wannan lokaci ba kasafai yak e janyo wata babbar matsalar kiwon lafiya ba.
Ko da yake wasu manyan matsaloli biyu kan janyo zuban jinni a watanni uku na farko, wato bari ko kuma ciki a bayan mahaifa.
Amma samun zuban jini a lokacin da ciki ya girma ya fi janyo damuwa, musamman idan matsala ce da ta shafi mabiyiya.
Biyu daga cikin manyan matsalolin da ke janyo zuban jini ga mai juna da cikinta ya fara tsufa su ne yadda mabiyiya ta kwanta a cikin mahaifa da kuma rabuwar mabiyiya da mahaifa tun lokacin hakan bai yi ba.
Masana a fannin kiwon lafiya sun ce girman mace wato matar da shekarunta suka haura 40 na daga cikin dalilan da ke sa mabiyiya ta kwanta ba a inda ya kamata ba a ciki.
Haka kuma haihuwa da yawa na sa wa mabiyiya ta kwanta a wurin da bai dace ba a cikin mahaifa.
A likitance dai kowace haihuwa da mace za ta yi mabiyiya na neman wajen da ba a taba kwanciya ba a cikin mahaifa ta kwanta.
Idan aka yi haihuwa da yawa mabiyiyar na komawa ta kwanta a kasan mahaifa, kuma hakan ka iya janyo zuban jini, idan ciki ya fara tsufa.
Zubar jini na iya jefa rayuwar jariri da na uwa cikin hadari, ko kuma a rasa shi gaba daya, musamman ma idan ciki ya girma.