Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya: Hirar BBC da Sheikh Ibrahim EL-Zakzaky
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Kimanin watanni takwas ke nan yanzu da wata babbar kotu a jihar Kaduna ta wanke jagoran ƴan Shi'a na harkar Islamiyya a Najeriya, Sheikh Ibrahim EL-Zakzaky da mai ɗakinsa daga dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masu inda kuma hakan ya kawo karshen zamansu a gidan yari na kimanin shekara shida.
Daga cikin tuhume-tuhumen da gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa Zakzaki, akwai haɗa taro ba bisa ka'ida ba da tayar da tarzoma da kuma kisa.
Wannan dai ya biyo bayan wani rikici tsakanin mabiya Elzakzaky da sojojin Najeriya, bisa zargin da sojojin suka yi wa mabiyansa na tare musu hanya a Zaria a 2015.
Sai dai bangaren Sheikh Zakzakin ya sha musanta wannan batu inda yake cewa gwamnati ta yi amfani da hakan ne domin far musu.
Kungiyar Amnesty International ta ce sakamakon wutar da sojoji suka buɗe kan mabiya Elzakzaky, mutum 345 ne suka mutu a lokacin.
Sheikh Ibrahim Elzakzaky, a hirarsa ta farko da ya yi da wata kafar yaɗa labarai ta Hausa tun bayan da aka sako shi, ya shaida wa shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko yadda al’amarin ya faru.