Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Muhimmancin samun hutu a rayuwar mata
Ku latsa lasifikar don sauraron shirin:
Mace tana bukatar ta samu lokaci na musamman da zata dinga hutawa saboda muhimmancin hakan ga lafiyarta.
Likitoci sun bayyana wasu hanyoyi wadanda mata za su dinga bi wajen kaucewa matukar gajiya a yayin ayyukansu na yau da kullum.
Sun kuma jadda muhimmanci cewa mace ta fara kulawa da kanta, domin ta yin haka ne za ta samu kuzari da walwala da koshin lafiyar kulawa da iyali da sauran wadanda ke da nauyi a kanta.
Wasu daga cikin hanyoyin sun hada da yin kebe lokaci na musamman na hutawa.
Haka zalika tsara yadda mace za ta yi ayyukanta zai taimaka wajen yin ayyuka masu ma'ana.
Sannan kai ziyara ga 'yan uwa da abokan arziki, zuwa wuraren shakatawa da yin abubuwan dake faranta wa mace rai suma suna taimakawa wajen rage matukar gajiya.
Matan da ke aiki ka'in da na'in ba tare da samun hutu kamar yadda ya kamata ba, na jefa rayuwarsu cikin hadarin rashin lafiya, a cewar likitocin.