Yakin Rasha da Ukraine: Illar makamin nukiliya ga ɗan Adam

An wallafa

Latsa hoton sama domin sauraren hirar

Batun yakin Rasha da Ukraine da ke ci gaba da ruruwa shi ne zancen da ya mamaye batutuwan da ake tattaunawa a duniya.

Abin da ya fi daukar hankalin jama'a kuma shi ne barazanar da shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi, cewa kasarsa ta kasance cikin shirin ko-ta-kwana wajen yiwuwar amfani da makaman nukiliya a yakin.

A shekarun 1945 ne dai lokacin yakin duniya na biyu Amurka ta yi amfani da makamin nukiliya a biranen Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da dubu 200, baya ga illar da har kusan yanzu biranen ke gani shekaru kusan 80 da wannan hari.

Shin ko yaya girman illar makamin na nukiliya ga dan adam? A filin Gane Mini Hanya Yusuf Yakasai ya tattauna da Farfesa Yusuf Aminu, shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Najeriya.