Ra'ayi Riga: Wancakali da dokokin bai wa mata dama ta musamman a majalisun Najeriya

An wallafa

A saurari shirin ra'ayi riga na wannan makon ta hanyar latsa alamar lasifika

A makon nan ne majalisun tarayyar Najeriya suka kada kuri'a a kan kudurorin yi wa tsarin mulkin kasar na 1999 garambawul.

Sassa sittin da takwas ne ciki har da batun bai wa shugabannin majalisun tarayya da cif joji-jojin kasar rigar kariya daga fuskantar shari'ah aka yi muhawara kansu.

Sai dai batun da ya fi daukar hankali shi ne yadda aka yi watsi da wasu kudirori biyar da suka shafi mata da suka hada da batun bai wa mata kashi 35 cikin 100 na shugabancin jam'iyyu , da samun kujeru na musamman a majalisun dojoki na johohi da tarayya, da kuma mukaman siyasa.

Lamarin ya fusata kungiyoyin mata har ta kai ga sun gudanar da zanga zanga a gaban majalisar a Abuja.

Ya kuke kallon wannan lamari? Me kuma kuke ganin ya sa majalisar ta yi fatali da bukatun matan?

Wannan shi ne batun da filin Ra'ayi Riga na wannan makon ya mayar da hankali kenan a kai.