Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Ko kun san gibin da ake da su wajen kula da masu cutar sankara?
Ku latsa hoton da ke kasa don kallon biidyon:
Taken ranar cutar sankara na bana (2022) shi ne 'Cike gibin da ke akwai wajen kulawa da masu cutar sankara' a duniya. Kuma babban asibitin Najeriya ya yi nazari a kan gibin da ake samu a kasar.
Likitoci a asibitin sun ce ana samun gibi wajen sanin alamomin cutar da gwaje-gwaje da rashin hali ko rashin samun asibitocin da suka dace dake bayar da kulawa.
Haka kuma tsofaffi ba sa samun damar kyakkyawan kulawa da kananan yara da rashin kudi da kuma rashin samun dawowa ganin likita bayan gashin farko.
Sannan ganin cewa kulawa da cutar daji na da tsada, mutane na hakura don abin hannunsu ya kare.
Haka zalika ga rashin issasun kwarrarun likitoci da ma'aikatan jinya ga matukar damuwar da masu cutar ke fadawa da kuma rashin samun wata kafa ta yi wa likitoci bayanin illolin da gashi ko alluran cutar kansa ke janyo wa masu cutar.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce a shekarar 2021 kawai an gano mutane miliyan 20 da ke fama da cutar kansa.
Yayin da mutane miliyan 10 suka mutu a sakamakon cutar.