Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mani Hanya tare da Alhaji Sule Lamido
Latsa hoton da ke sama domin sauraren hira da Alhaji Sule Lamido:
Duk da cewa a hukumance ba a kada gangar siyasar zaben shekarar 2023 ba a Najeriya, tuni wasu masu son tsayawa takara suka soma gudanar da taruka da gagganawa.
Har yanzu dai za a iya cewa jam’iyyun na ta tattaunawa da kuma yin sulhu a tsakanin ‘ya’yansu.
Jam’iyyar PDP, wadda ita ce babbar jam’iyyar hamayya a kasar, ita ma har yanzu na yin zagaye wurin tsoffin jiga-jiganta kamar irin su tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo.
Khalipha Dokaji ya tattauna da Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa kan halin da ake ciki a jam’iyyar, inda ya tambaye shi ko zai yi takara a 2023?