Gane Mani Hanya da Senata Ahmed Sani Yarima 22/01/2022

An wallafa

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Senata Ahmed Sani Yarima ya sake ayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben badi.

Senata Yarima wanda tun a shekara ta 2007 ya fara fitowa takarar shugabancin kasar ya yi watsi da tsarin karba-karba a zaman abin da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar duk da cewar ana ganin lokaci ne da ya kamata yankin kudancin kasar ya fitar Shugaban kasa na gaba.

A filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon ya bayyana wa abokin aikinmu Haruna Shehu - Tangaza dalilansa na nace wa kan neman shugababancin kasar da kuma matsayinsa game da rikicin shugabancin da jam'iyyar tasa ke fama da shi a jiharsa ta zamfara.